22 Mayu 2022 - 19:20
Shugaban Gwamnatin Jamus Ya Fara Wani Ran-gadi A Afrika

Shugaban gwamnatin kasar Jamus, Olaf Scholz, ya fara wata ziyara a Afrika wacce ta kai shi kasashen Senegal, Nijar da kuma Afrika ta Kudu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Yayin ziyarar wacce zai kaddamar daga Senegal yau Lahadi, wazirin kasar ta Jamus, Olaf Scholz, zai tattauna batutuwan da suka shafi huldar tattalin arziki da kuma tsaro.

A Nijar Mista Scholz, zai ziyarci sojojin Jamus dake kasar.

Daga Nijar, shugaban gwamnatin kasar ta Jamus, zai karkare ziyarar tasa da Afrika ta Kudu.

342/